A yau a Alhamis 25 ga watan shawwal ita ce ranar shahadar Imam Sadik (a) jikin manzon Allah (s) kuma limami na 6 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s).
Imam Ja'afar bin Muhammad wanda ya fi shahara da Imam Sadiq (a) yana daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s) wadanda suka sami damar yaɗa addinin musulunci wanda kakansa Annabin Rahama(Sawa) ya zo da shi. Da shi da mahaifinsa Imam Muhammad Al-baqir (a) sun bude jami'a mafi girma a madina a zamaninsu.
Malaman tarihi sun bayyana cewa Imam Sadik (a) yana da dalibai kimani 4000 wadanda suka dauki ilmi a wajensa, a fannonin ilmi da dama.
Ja'afar bn Muhammad, wanda aka fi sani da Imam Ja'afar Sadik (AS) (83-148H), shi ne limami na shida kuma ya jagoranci ‘yan Shi’a na tsawon shekaru 34 (114 zuwa 148 bayan hijira), wanda ya yi daidai da halifancin halifofin Umayyawa biyar na karshe, tun daga Hisham bn Abdulmalik, da kuma halifofin Abbasiyawa biyu na farko, Saffah da Mansur Dwaniqi. Saboda raunin gwamnatin Banu Umayyawa Imam Sadik (AS) ya fi sauran Imaman Shi'a aiki wajen yaɗa ilimi. An kiyasta adadin almajiransa da masu ba da ruwayoyinsa da suka kai 4,000. Yawancin ruwayoyin Ahlul Baiti (a.s.) sun fito ne daga Imam Sadik (a.s.), don haka ake kiran mazhabar Imamiyya ta Shi'a da sunan Ja'afari.
Haka nan Imam Sadik (AS) yana da matsayi mai girma a cikin shuwagabannin jagororin fiqihu Ahlus-Sunnah. Abu Hanifa da Malik bn Anas sun ruwaito daga gare shi. Abu Hanifa ya dauke shi mafi ilimi a cikin musulmi.
Shahadarsa:
Sheikh Saduq ya bayyana cewa Imam Sadik (a.s.) ya yi shahada ne bisa umarnin Mansur Dawaniqi da ba shi guba. Ibn Shahr-e-Ashhub ma ya bayyana irin wannan ra’ayi a cikin Manaqib da Muhammad ibn Jarir al-Tabari na uku a cikin Daala’il al-Imamah. An dogara da shahadarsa ne akan wannan ruwayar “Wallahi ba mu ɗaya daga cikinmu sai dai an kashe shi ko yayi shahada ne”. Shi kuwa Sheik Mufid ya yi imani da cewa babu gamsasshiyar hujjar shahadarsa. Sayyid Ja’afar Murtaza Ameli masanin tarihi ya dangana maganar Sheikh Mufid ga Taqiyyah. Kabarinsa yana cikin makabartar Baqi’a kusa da kaburburan kakanninsa, Imam Bakir, Imam Sajjad, da Imam Hassan.
Muna mika ta'aziyyarmu ga dukkan musulmi musamman mabiya mazhabar Jaafariya dangane da wannan babban rashin da fatan Allah ya bamu cetonsu ranar da babu mai ceto sai da izinin Allah
Your Comment